Rasha Ta Hallaka Wasu Jiga-jigan Da'esh A Siriya

Rasha Ta Hallaka Wasu Jiga-jigan Da'esh A Siriya

Rundinar sojin kasar Rasha ta sanar da hallaka wasu mayan kwamandojin kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a yankin Deir Ezzor na kasar Siriya.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha ta fitar a yau Juma'a ta ce daga cikin wadanda aka hallaka har da kwamandan yaki na kungiyar da akewa lakabi da ministan yaki cewa da Goulmourod Halimov, da kuma jagoran kungiyar ta Da'esh a yakin na Deir Ezzor Abou Mohammed al-Chemali.

A cewar sanarwar mutanen biyu na daga cikin mayan 'yan ta'addan da Amurka ta ke nema ruwa a jallo, har ma ta sanya ladan kudi akansu.

Dukkan su dai sun hallaka ne a hare haren da jiragen yakin Rashar suka kai a yayin da sojojin Siriya suka kusa kai a yankin na Deir Ezzor a ranar Talata data gabata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky