Rasha Ta Bukaci Tsagaita Wuta A Syria Daga Ranar Talata.

Rasha Ta Bukaci Tsagaita Wuta A Syria Daga Ranar Talata.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya umarci a dakatar da barin wuta na wani lokaci duk rana daga gobe Talata a yankin ‘yan tawaye na gabashin Ghouta dake kasar Syria saboda asamu a kai dauki.

Wannan umarnin tsagaita wuta, Ministan Tsaro na Rasha  Sergei Shoigu  ya sanar inda yake cewa daga gobe Talata za’a sami sassauci na tsagaita wuta tsakanin karfe  tara zuwa biyu na rana, saboda a samu a kai tallafi ga mabukata.

Tun da fari a yau littini shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Turkiya Recep Tayyip Erdogan sun tattauna batun Syria ta wayan talho inda suka nemi a tsagaita wuta a yakin na Syria kuma lallai a hada da yankin Afrin inda Turkiya ke ta barin wuta kan kurdawa

Shugaban Faransa ya fadi cewa tsagaita wutan na tsawon kwanaki 30 ya hada da dukkan sassan Syria wato har da yankin Afrin.

A yau din nema Gwamnatin Turkiya ke fadin cewa ta tura karin Dakaru domin yakin sosai a yankin na Syria.

Shima dai Babban Sakatare Janar na MDD Antonio Gutteresh wanda yake jawabin bude taro karo na 37 na Hukumar kare hakkin dan-adam ta MDD a Geneva ya nemi lallai a tsagaita wutan

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky