MDD : Yemen Na Fuskantar Babbar Barazanar Yunwa

MDD : Yemen Na Fuskantar Babbar Barazanar Yunwa

MDD ta nuna damuwa matuka akan halin da ake ciki kan matsalar kamamcin abunci a kasar Yemen.

Mukadashin sakatare janar na MDD mai kula da ayyukan jin kai, Stephen O'Brien ya bayyana a zauren kwamitin tsaro na MDD da matsalar wacce ta kasance mafi muni a duniya.

Wakilin MDD kan rikicin kasar Yemen,  Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ya bayyana a zauren kwamitin tsaro na MDD cewa yaki da ake fama da shi a yemen ya ruguza kashi 4% na muhallai jama'a a yankin Mokha.

Kimanin Miliyan bakwai nan al'ummar Yemen na fama da yunwa a yayin da kuma cutar kwalera a kashe mutane 500 a wannan kasa. 

Mafi yawa daga cikin wadanda wannan iftila'in yafi shafa yara kanana ne. 

MDD ta bukaci bangarorin dake rikici a kasar dasu gaggauta samar da hanyoyin da zasu kai ga isar da kayan agaji ga mabukata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky