Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Ce: Mahukuntan Saudiyya Ne Suka Tilastawa Sa'ad Hariri Yin Murabus

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Ce: Mahukuntan Saudiyya Ne Suka Tilastawa Sa'ad Hariri Yin Murabus

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Mahukuntan Saudiyya ne suka tilastawa Sa'ad Hariri yin murabus daga kan mukaminsa na fira ministan Lebanon, kuma hakan babban cin mutunci ne ga fira ministan da ma dukkanin al'ummar Lebanon.

A jawabin da ya gabatar a jiya Juma'a a zaman taron juyayin cikan ranaku arba'in na jikan manzon Allah Imam Husani {a.s} kuma ranar tunawa da shahidan kungiyar Hizbullahi ta Lebanon: Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewa: A halin yanzu dukkanin al'ummar Lebanon da ma duniya sun kai ga tabbacin cewa: Mahukuntan Saudiyya suna tsare ne da Sa'ad Hariri kuma tilasta masa suka yi kan yin murabus daga kan mukaminsa na fira ministan Lebanon. Kamar yadda suke son gabatar da wani mutum na daban a matsayin sabon fira ministan kasar.

Har ila yau Sayyid Hasan Nasrullahi ya fayyace cewa: Murabus din Sa'ad Hariri kan mukaminsa na fira ministan Lebanon baya kan doka domin tilasta masa aka yi, sakamakon haka al'ummar Lebanon suna daukansa a matsayin fira ministan kasarsu mai halacci.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullahi ya kuma kara da cewa: Mahukuntan Saudiyya suna kokarin zaburar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Lebanon. Kamar yadda mahukuntan Saudiyya da Amurka su suka kafa kungiyar ta'addanci ta Da'ish tare da daukan nauyin kungiyar a wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky