Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami

Kasar Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzami, a cewar jami'an Koriya Ta kudu da Amurka.

Sun ce makamin ya tarwatse jim kadan da harba shi - karo na biyu kenan a mako biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Koriya ta Arewa da nuna "rashin da'a" ga China da shugabanta.

An harba makamin ne ranar Asabar daga kudancin Pyeongan, a cewar Koriya ta Kudu.

Mr Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Koriya ta Arewa ta nuna rashin da'a ga bukatun China da shugabanta da ke da kima inda ta harba makami mai linzami a yau, ko da yake bai yi nasara ba. Hakan babu dadi."

A kwanan baya ne Mr Trump ya barki bakuncin shugaban China Xi Jinping inda ya yabe shi kan abin da ya kira "kokarin da kake yi matuka" kan Koriya ta Arewa.

An harba makami mai linzamin da bai yi nasara ba ne sa'o'i kadan bayan kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya tattauna kan shirin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky