Korea Ta Arewa ta yi watsi da sabbin takunkumai

Korea Ta Arewa ta yi watsi da sabbin takunkumai

Korea Ta Arewa ta shure jerin sabbin takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta sa ke kakaba ma ta saboda ci gaba da gwaje-gwajenta na makaman Nukiliya.

A fusace ne dai, Korea Ta Arewa ta mai da martani a wannan Litinin game da sabbin takunkuman da aka malkaya ma ta, in da ta ke ta ce, ihu ne bayan hari domin babu wani dalili ko barazana da zai hana ta ci gaba da shirinta na Nukiliya duk da barazanar da Amurka ke yi ma ta.

A karon farko kenan da Korea ta mayar da martani tun bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya ma ta sabbin takunkuman a karshen mako, abin da ake ganin zai haifar ma ta da asarar akalla Dala biliyan 1 a kowacce shekara.

Wata sanarwa da hukumomin Korea ta Arewa suka bai wa Kamfanin Dillancin Labaran kasar a yau, na cewa dukkan wani takunkumi ya saba wa ‘yancinta, saboda haka ba gudu ba ja da baya kan abin da ta sanya a gaba.

A cewar sanarwar, Amurka za ta gane kurenta saboda tsayawa kai da fata don ganin an sake malkaya ma ta takunkumi.

Kasar China mai makwabtaka da  Korea ta Arewa ta ce,  za ta mutunta sabbin takunkuman.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky