Kasashen Larabawa Sun Goyi Bayan Samar Da Kasashen Isra'ila Da Palestine

Kasashen Larabawa Sun Goyi Bayan Samar Da Kasashen Isra'ila Da Palestine

kungiyar kasashen larabawa ta ce tana goyan bayan samar da kasashen Palestine da kuma Isra'ila domin kawo karshen dadaden rikici na tsakanin bangarorin biyu.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wani daftarin kudiri da kungiyar zata gabatar a babban taronta na shekara-shekara a gobe Laraba.

Ministocin kasashen larabawa da suka hadu tun ranar Litini a birnin Sweimeh sun nuna matukar goyan bayansu akan samar da kasashen biyu wanda zai baiwa Palestine yancin cin gashin kanta akan yankuna da aka mamaye mata tun cikin shekara 1967 ciki har da yankin gabashin Kudus.

Daftarin kudirin wanda kamfanin dilancin labaren AFP ya samu irinsa, ya kuma bukaci dukkan kasashen duniya dasu mutunta kudirin kwamitin tsaro na MDD dake adawa da ci gaba da mamayar da mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila ke yi al'ummar Palastine da kuma kin amuncewa Isra'ila mayar da offisoshin jakadancinta wuri zuwa birnin Qudus mai tsarki.

Samar da kasashen Palestine da Isra'ila shi ne dai galibin kasashen duniya ke fata, saidai batun na fuskanci koma baya sakamakon zuwan sabuwar gwamnatin Donald Trump na Amurka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky