Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kai Jerin Hare-Hare Kan Lardin Hudaidah Na Kasar Yamen

Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kai Jerin Hare-Hare Kan Lardin Hudaidah Na Kasar Yamen

Rundunar kawancen Saudiyya ta kaddamar da jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankunan lardin Hudaidah da suke yammacin kasar Yamen.

Kafar watsa labaran Sputnik ta kasar Rasha a yau Juma'a ta watsa labarin cewa: Jiragen saman yakin rundunar kawancen Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankunan lardin Hudaidah da ke yammacin kasar Yamen, inda jiragen suka kai hare-hare har sau uku kan yankin Azzubaidah da Addiraihami da kuma Zubaid.

Har ila yau jiragen saman yakin rundunar kawancen na Saudiyya sun yi luguden wuta kan ofishin 'yan sanda da kuma gidajen jama'a da suke yankin Attahrir a lardin na Hudaidah amma ya zuwa yanzu babu labarin irin hasarar da hare-haren suka janyo.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky