Hukumar "UNICEF" Ta Bukaci Daukan Matakin Kare Kananan Yara A Kasar Siriya

Hukumar

Asusun Kula da Kananan Yara da Mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ta bukaci duniya ta dauki matakin kare kananan yara daga irin masifar da suke fuskanta a kasar Siriya.

A bayanin da babban daraktan gudanarwa a Hukumar "UNICEF" Anthony Lake ya fitar yana dauke da cewa: Harin ta'addancin da aka kai kan tawagar fararen hula a kusa da garin Halab da ke arewacin kasar Siriya a ranar Asabar da ta gabata, fiye da kananan yara 60 ne suka rasa rayukansu, lamarin da ke kara fayyace irin tsananin bukatar da ake da ita a fagen kara matsa kaimi domin kare kananan yara a kasar ta Siriya da ke fama da tashe-tashen hankula.

Anthony Lake ya kara da cewa: Tashe-tashen hankulan da suke ci gaba da gudana a kasar Siriya yau tsawon shekaru shida, ana ci gaba da tafka laifukan yaki musamman a kan mata da kananan yara.

A ranar Asabar da ta gabata ce dai aka kai harin wuce gona da iri kan wata motar bus da take dauke da fararen hula al'ummun yankunan Fo'ah da na Kufriyah da suke gundumar Rashidain a garin Halab, inda harin ya lashe rayukan mutane 126 kuma 68 daga cikinsu kananan yara.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky