Harin bam ya kashe mutane 24 a Kabul

Harin bam ya kashe mutane 24 a Kabul

Wani harin bam ya yi sanadiyyar mutuwar mtuane 24 tare da raunata wasu 42 a birnin Kabul na kasar Afghanistan a sanyin safiyar yau Litinin.

An kai harin ne akan wata motar bas da ke dauke da ma’aikata da ke kan hanyarsu ta zuwa aikin safe, kamar dai yadda Najib Danish mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida ya kasar.

Tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin farmakin wanda aka kai kan ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatar ma'adinai.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, harin ya yi muni matuka domin kuwa sai dai da ya kusan ruguza ma sa gida


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky