Dakarun Kasar Yamen Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Sojin Saudiyya

Dakarun Kasar Yamen Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Sojin Saudiyya

Sojojin Yamen da dakarun sa- kai na kasar sun yi luguden wuta kan sansanin sojin Saudiyya da ke lardin Jizan na kasar ta Saudiyya.

Rundunar sojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar a yau Laraba sun yi luguden wuta kan sansanin sojin masarautar Saudiyya da ke lardin Jizan a kudancin kasar Saudiyya a matsayin maida martani kan harin da sojojin Saudiyya suka kaddamar kan lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen.

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojin Yamen da dakarun sa-kan sun yi nasarar tarwatsa tankokin yaki, motoci masu silke, makamai masu linzami da sauransu da suke sansanin na sojojin Saudiyya lamarin da ya firgita mahukuntan Saudiyya.

Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa- kai na kasar sun kai wasu jerin hare-haren daukan fansa da makamai masu linzami kan sansanin sojin Saudiyya da na kawayenta 'yan mamaya a yankin Al-Mukha da ke yammacin Saudiyya, inda hare-haren suka yi sanadiyyar halakar sojoji masu tarin yawa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky