Bahrain: An Kai Ayatollah Sheikh Isa Qasim Asibiti

Bahrain: An Kai Ayatollah Sheikh Isa Qasim Asibiti

An kai babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Qasim asibiti a safiyar yau, sakamakon rashin lafiyar da ya fama da ita.

Shafin yada labarai na Lu'alua ya abyar da rahoton cewa, a yau ne iyalan babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Qasim suka dauke zuwa asibiti, sakamakon matsalolin ciwon suga da hawan jini mai tsanani da yake fama da su.

Mahukuntana masarautar kama karya ta kasar Bahrain sun bayar da dama ga iyalan malamin da su dauke shi zuwa asibiti a yau, bayan tsare shi cikin gida na tswon lokaci, tare da hana shi ganawa da jama'a.

Al'ummomin kasar Bahrain da ma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun gargadi mahukuntan masarautar kama karya ta Bahrain dangane da makomar malamin, sakamakon hana kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, wanda hakan yasa ala tilasta masarautar ta bayar da dama daukar malamin zuwa asibiti.

masarautar kama karya ta Bahrain ta killace gidan shehin malamin ne sakamakon kiran da yake ga mahukuntan kasar kan su baiwa kowane dan kasa hakkinsa  amatsayinsa na dan kasa, ba tare da tauye hakkin wani bangare ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky