Arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu da jami’an tsaro a India

Arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu da jami’an tsaro a India

An samu arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra’ayi da jami’an tsaro a arewacin kasar India, bayanda fusatattun masu zanga-zangar suka yi barazanar kai wa gidajen Cinema hare-hare a sassan kasar, idan suka haska Fim din Padmavati da kotun kolin kasar ta bada umarnin saki.

Mabiya addinin Hindun na kallon Fim din a matsayin cin zarafi a garesu bisa yadda aka nuna soyayya tsakanin wata sarauniyar Hindu da wani Muslmi basarake.

‘Yan Sanda da sauran jamian tsaro sun karfafa tsaro a gidajen sinima tun ajiya saboda fargaban kazamin bore.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky