Ana kwashe 'yan tawaye da iyalansu daga garuruwan gabashin Ghouta

Ana kwashe 'yan tawaye da iyalansu daga garuruwan gabashin Ghouta

Mayakan ‘yan tawayen Syria suna ci gaba da ficewa daga garuruwan yankin gabashin Ghouta tare da iyalansu, bayan da sojojin gwamnati suka yi nasarar mamaye mafi akasarin yankin

A daren ranar Asabar jerin gwanon manyan motoci suka fara aikin kwashe mayakan da iyalansu, bayan cinmma yarjejeniya tsakanin ‘yan tawayen da gwamnati.

Zuwa yanzu kusan kashi 90 na yankin gabashin Ghouta yana hannun sojin Syria, birnin Douma kadai ne a halin yanzu yake hannun, ‘yan tawayen.

Rahotanni sun ce suma ‘yan tawayen kungiyar Jaish al-Islam, da ke iko da Douma, suna kan tataunawa da gwamnati, domin mika mata birnin


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky