An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh

An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh

n zartar da hukuncin kisa a kan jagoran kungiyar Jihad Islami a kasar Bangaladesh bisa zargin bude wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar wuta.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, ministan cikin gida na kasar Bangaladesh Asadu Zaman Khan ya sanar da cewa, an zartar da hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhanan, jagoran kungiyar Jihad Islami, tare da wasu mutane biyu na hannun damarsa, bisa samunsu da hannu a harbin da aka yi wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh.

Tun kimanin shekaru 12 da ska gabata ne dai ‘yan kungiyar ta Jihad Islami suka budewa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh wuta, amma bas u samu damar kasha shi, sai dai jami’an ‘yan sanda 3 sun rasa rayukansu,yayin da wasu mutane 79 suka samu raunuka.

Tun a cikin shekara ta 2014 ne dai wata kotu ta yanke hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhannan tare da wasu na hannun damarsa, tare da yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu 6 daga cikinsu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky