An kai harin kunar bakin wake a masallacin 'yan Shi'a a Kabul

An kai harin kunar bakin wake  a masallacin 'yan Shi'a a Kabul

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun tada bam a wani Masallachin mabiya mazhabar Shi’a da ke Kabul na kasar Afghanistan, inda suka kashe mutane 4 suka kuma jikkata wasu da dama.

Najib Danish, mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar, ya ce an kai harin ne a Masallachin Al Zahra da ke yammacin birnin na Kabul.

Kungiyar 'yan ta'addan ISIS ta dauki alhakin kai harin, wanda shi ne irinsa na farko da aka kai wa masallacin da mabiya mazhabar ta Shi’a ke ibada cikinsa a wannan wata na Ramadan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky