An gargadi Gwamnatin Bahrain Akan Sheikh Issa Kasim

An gargadi Gwamnatin Bahrain Akan Sheikh Issa Kasim

Kungiyar gwgwarmaya Musulunci ta Kasar Iraki "Haraktun-Nujaba'a' ta gargadi gwamnatin Bahrain akan duk wani yunkuri na cutar da babban malamin addinin kasar Sheikh Isa Kasim.

Kungiyar gwgwarmaya Musulunci ta Kasar Iraki "Haraktun-Nujaba'a' ta gargadi gwamnatin Bahrain akan duk wani yunkuri na cutar da babban malamin addinin kasar Sheikh Isa Kasim.

Babban magatakardar kungiyar 'Harkatun-Nujaba'a' Akram al-Ka'aby, wanda tashar telbijin din "Ku'u-lu'a' ta yi hira da shi, ya ce; "Sheikh Isa Kasim, ba malamin kasar Bahrain ba ne kadai, don haka cutar da shi da masu mulki na ali-Khalifah za su, yi ya shafi mabiya mazhabar ahlul-bayti (a.s.).

Babban magatakardar kungiyar gwgawarmayar ya kuma gargadi masu mulkin kasar ta Bahrain akan ci gaba da mika kai ga ali-Sa'ud da kuma aiwatar da umarninsu, domin a karshe reshe zai juye da mujiya.

Tun a 2011 kasar Bahrain ta ke cikin mawuyacin hali ta fuskar tsaro da siyasa saboda murmushe al'ummar kasar masu  son kawo sauyi ta hanyoyin lumana. Daruruwan mutanen kasar ne dai su ke cikin kurkuku yayin da wasu da dama su ka rasa rayukansu.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky