A Yau Ne Kwamitin Tsaron MDD Zai Kada Kuri'a Kan Kara Kakaba Wa Syria Takunkumi

A Yau Ne Kwamitin Tsaron MDD Zai Kada Kuri'a Kan Kara Kakaba Wa Syria Takunkumi

Kwamitin tsaron majalisar dinkin na shirin gudanar da wani zama a yau domin kada kuri'a kan kakaba wa gwamnatin Syria wasu sabbin takunkumai, bisa zargin da wasu kasashen turawa suka mata na cewa ta harba makamai masu guba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kasashen Amurka, Faransa, da kuma Birtaniya ne suka gabatar da wannan daftarin kudiri, wanda za a kada kuri'a a kansa a zaman da kwamitin tsaro zai gudanar a yau Talata.

To sai dai a nata bangaren kasar Rasha, wadda mamba ce ta din-din-dina  kwamitin tsaron, ta sha alwashin hawar kujerar naki a kan wannan daftarin kudiri.

Sakamakon sabani na siyasa da kasashen Amurka, Birtaniya gami da Faransa suke da shi da gwamnatin Syria, sun taka gagarumar wajen yin amfani da wasu sarakunan larabawa domin rusa kasar Syria, ta hanyar yin amfani da 'yan ta'adda masu da'awar jihadi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky