A Siriya 'Yan Ta'adda Sama Da Dubu Ne Suka Ficce Daga Lardin Idlib

A Siriya 'Yan Ta'adda Sama Da Dubu Ne Suka Ficce Daga Lardin Idlib

Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta tabbatar da cewa; adadin 'yan ta'addar da su ka fice daga Idlib sun haura 1000

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta sanar da cewa; A halin da ake ciki a yanzu Moscow da Ankara suna tuntubar juna domin tabbatar da cewa; yan ta'addar sun ci gaba da ficewa daga yankin Ha'il da ke gundumar Idlib.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiya kuwa ta sanar da cewa; A yanzu an fara samar da yankin da za a kwance damarar yaki a cikinsa a Ha'il, kuma na tsaida lokacin da za a kawo karshen ficewar 'yan ta'addar tare da manyan makamansu.

Idlib ne gunduma daya tito da ta yi saura a hannun 'yan ta'adda a duk fadin kasar Syria.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky