Sake Watsi Da Dokar Trump, Kan Hana Musulmai Shiga Amurka

Sake Watsi Da Dokar Trump, Kan Hana Musulmai Shiga Amurka

Sa'o'i kadan kafin sabuwar dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa hannu ta hana musulman wasu kasashe shida shiga kasar ta fara aiki, wani akalin kotun tarraya ya yi wasti da dokar.

Alkalin kotun ta Hawaï, Derrick Watson, ya ce soke dokar zai kaucewa Amurka tafka babban kuskure. 

Shugaban kasar Donald Trump wanda ke bayyani a wani taro a birnin Nashville dake kudancin kasar, ya kalubalanci matakin kotun wanda ya danganta da kaucewa hanyoyin shari'a wanda ba'a taba yin irinsa ba a kasar.

Mista Trump ya kuma lashi takobin kalubalantar hukuncin a duk inda ya dace har zuwa kotun koli, wanda a cewarsa domin kare 'yan kasarsa.

Shi dai alkali Watson, ya dogara ne akan wasu kalaman Trump, akan musulmai wanda ya ce akwai abubuwa da dama dake nuna kyammar musulmai.

Alkalin dai na la'akari ne da kalaman Trump a lokacin yakin neman zabensa, a lokacin da ya yi firici akan hana musulmi sanya kafa a Amurka muddun ya ci zabe.

Da misalin karfe 12 na daren Jiya Laraba ne ya kamata sabon kudirin da Donal Trump ya rattabawa hannu a karo na biyu bayan aiwatar da wasu sauye sauye dake hana musulmin wasu kasashe shiga Amurkar ya kamata ya fara aiki.

Wata kungiyar lauyoyin jihohin Amurka ce dai ta shigar da wannan kara kuma ta samu nasara.

Lauyoyin dai sun ce hana musulmai shiga Amurka kan iya haifar da wariya da karamcin samun ma'aikata da kuma haifar da koma baya a fannin yawon bude ido na kasar.

Wannan matakin na kotun Hawai, na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kungiyoyin kare yanci da bakin haure a lardin Greenbelt, dake birnin Maryland a gabashin kasar ciki har da babbar kungiyar nan ta (American Civil Liberties Union) ke ci gaba da sukan matakin na Mista Trump wanda a cewarsu na nuna wariya ne ga musulmi.

Lauyan kungiyar ta (ACLU) mai suna Omar Jadwat, ya ce hadarin dake tattare da matakin na Trump ga musulmi daidai yake ga 'yan gudun hijira.

Kungiyar ta (ACLU) tayi maraba da matakin kotun wanda a cewarta ya sake dakatar da kudirin na Trump wanda abun kunya ne.

Gwamnatin Amurka dai nada damar daukaka kara akan wannan matakin na kotun ta Hawai.

Shi dai sabon kudirin a cewar gwamanatin Amurka baya da nufin nuna wariya akan addinai, hasali ma na kare al'ummar kasar ne.

Sabon kudirin da shugaba Trump ya sanyawa hannu wanda kotu ta sake watsi da shi a karo na biyu, ya tanadi rufe iyakokin kasar ta Amurka na wani dan lokaci ga illahirin 'yan gudun hijira na duniya tare da dakatar da bada takardar Visa) na tsawan kwanaki 90 ga 'yan kasashen da suka hada da Iran, Libya,Syria, Somaliya,Sudan da kuma Yemen.

Kudirin na farko dai ya hada da kasar Iraki, saidai aka cire ta daga jerin wadanan kasashen bayan kawo gyaren fuska a wancen kudirin bayan da wani alkalin kotu a birnin Seattle ya dakatar da shi.

Tun dai bayan harin 11 ga watan Satunban 2001, duk jerin hare hare mafi muni da aka kai a kasar, Amurkawa ne suka kaisu, lamarin da ya nuna cewa babu daya daga cikin mutanen jerin kasashen da wannan kudiri ya shafa da suka da hannu a wani hari cikin Amurka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky