Sabon Makami: Amurka Ta Gargadi Koriya Ta Arewa

Sabon Makami: Amurka Ta Gargadi Koriya Ta Arewa

Bayan gwajin wasu makamai masu dogon zango da Koriya Ta Arewa ta yi, Amurka ta sake yi ma ta kashedi ta cewa daina shirin daukar Dala ba gammo saboda ba za ta lamunta da ganin makamai masu hadari a hannun kasa irin Koriya Ta Arewa ba.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta yi gargadi jiya Laraba cewa, gwajin makami mai linzami da ke iya isa wata kasa da Koriya ta arewa ta gudanar na baya bayan nan dake cike da takaddama, ya kara sa duniya kusantar yaki.

Ta kara da cewa, “idan har aka shiga yaki, ku sani, za a rusa gwamnatin Koriya ta Arewa babu ko tantama”.

Ta kuma yi kira ga kasashen da ke cikin kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya su yanke hulda da gwamnatin Koriya Ta Arewa Mai Fada a Pyongyang. Ta ce “ya kamata dukan kasashe su katse huldar jakadanci da Koriya ta Arewa su kuma takaita dangantakar soji da ta kimiya da fasaha da kasuwanci da kasar.

Haley ta ce, shugaba Donald Trump ya shaidawa takwaran aikinsa na kasar China Xi Jinping ta wayar tarho cewa, lokaci ya yi da ya kamata Beijing ta daina sayar wa Koriya ta arewa mai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky