Rikicin Venezuela: An Ja Daga Tsakanin Shugaba Maduro Da 'Yan adawa

Rikicin Venezuela: An Ja Daga Tsakanin Shugaba Maduro Da 'Yan adawa

An ja daga tsakanin gwamnatin Venezuela da 'yan adawan kasar yayin da ranar da shugaba Nicolas Maduro ya ware domin zaben 'yan majalisa ta musamman da za su sauya kundin tsarin mulkin kasar ke karatowa, matakin da 'yan adawan suka ce ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa.

‘Yan adawa a kasar Venezuela sun ba da sanarwar fara zanga-zangar kwanaki biyu a cikin wannan makon domin tursasa wa shugaba Nicholas Maduro ya soke zaben nan da ya kudiri aniyar yi a ranar 30 ga wannan watan domin zaben ‘yan majalisa.

Masu adawar sun "muna kira ga daukacin jama’ar kasa, da kungiyoyi da su shiga cikin yajin aiki na sa’o’i 48 a ranar laraba da alhamis," kamar yadda dan majalisar dokokin Simon Calzadilla ke cewa.

Calzadilla ya ce zanga-zanga za ta biyo bayan yajin aikin a ranar juma'a inda za a bukaci Maduro da ya soke wannan batun zaben a hukumance.

Sai dai shugaban ya yi kememe duk da karuwar zanga-zangar da ake samu a kasar dama kiraye-kiraye daga sassan duniya daban-daban kan shawo kan rikicin ta hanyar sasantawa da 'yan adawan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky