Musulmi da Krista da Yahudawa sun yi buden baki

Musulmi da Krista da Yahudawa sun yi buden baki

Musulmi da Kirista da Yahudawa da Kwabadawa da mabiya addinin Buda da kuma Sikh sun zauna tare suka tattauna da juna wajen cin abinci.

Allen wani wanda wannan ne shigarshi masallaci karon farko ya bayyana cewa, mutane da dama kamarshi basu fahimci al’ummar Musulmi ba.

Yace watanni da suka shige, membobin majami’arsu suma sun shiga sahun wadansu wajen bayyana fushinsu da rashin gamsuwa da kuma kiyayya da suke da ita a kan dabi’un wadansu addinai.

Yace amma, da na zauna ina sauraron bayanan sai nayi tunani cewa, menene za a yi da irin wannan?

Allen yace, mafitar itace a yi kokarin samar da wani dandanlin tattaunawa da ya kunshi mabiya addinai dabam dabam, abinda za a fara da kaka. Ta yadda za a hada kan mutane mabiya addinai dabam dabam, da zai taimakemu mu fahimci inda ra’ayoyinmu suka zo daya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky