Dokar haramtawa baki Musulmi shiga Amurka zata fara aiki

Dokar haramtawa baki Musulmi shiga Amurka zata fara aiki

Kotun Kolin Amurka ta bai wa shugaba Donald Trump damar aiwatar da wani bangare na dokar haramta wa wasu kasashen musulmi shiga cikin kasar.

Matakin kotun yana a matsayin nasara ga Trump, wanda ya sha nanata cewa, dokar tana da muhimmanci don kare kasar daga barazanar ta’addanci.

Jim kadan da yake hukuncin Kotun Kolin kasar ta Amurka, shugaba Donald Trump ya ce, hukuncin ya bada damar haramta wa ‘yan kasashen Musulmin shida da ka iya brazanar ta’addanci ga Amurka, shiga kasar.

Trump ya ce, a matsayinsa na shugaban kasa, ba zai amince wa wasu mutane da ka iya cutar da Amurka ba.

Kotun kolin ta ce, dokar wadda wata karamar kotu ta soke ta a can baya, za a iya amfani da ita har na tsawon kwanaki 90, wajen dakatar da mutanen wadannan kasashe shida da ba su da alaka da wani a Amurka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky