Ziyarar Shugaba Buhari A Garin Dapchi

Ziyarar Shugaba Buhari  A Garin Dapchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar, inda aka sace 'yan matan sakandare fiye da 100 a watan da ya gabata.

Shugaban ya gana da iyayen yaran da aka sace a makarantar sakandaren, inda a nan ne aka sace 'yan matan.

Gwamnati ta sha suka kan yadda ta tunkari sace 'yan makarantar, wanda aka hora alhakinsa kan kungiyar Boko Haram.

Ziyarar wani bangare ne na rangadin da ya ke yi a jihohin da ke fama da rikice-rikice a kasar.

Tun da safiyar Larabar ne Shugaba Buhari ya isa Damaturu, babban birnin jihar Yobe inda gana da shugabannin al'umma da sarakunan gargajiya.

Tuni dai iyaye a garin Dapchi suka yi dafifi a makarantar da aka sace 'ya'yan nasu inda suke jiran isar Shugaba Buharin don ganawa

Wani daga cikin iyayen yaran ya shaida wa BBC cewa: "Muna jira ne shugaban ya zo ya gamsar da mutanen gari kan kokarin da gwamnati ke yi na ceto 'ya'yansu da kuma matakan da za a dauka don hana sake afkuwar irin hakan."

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata sama da 100 daga makarantar sakandaren Dapchin kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Sace 'yan matan na Dapchi, wanda ya zo shekara hudu bayan sace 'yan matan Chibok, ya tayar da hankalin mazauna garin da ma jihar baki daya.

Kuma ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke cewa ta karya lagon mayakan na Boko Haram.

A ranar Litinin ne tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce kasarsa na aiki tare da Najeriya domin ganin an kubutar da 'yan matan.

Shi dai Shugaba Buhari ya ce ba ya so a yi amfani da karfin tuwo domin kada a jefa rayukan yaran cikin hadari, a don haka a shirye yake ya tattauna da wadanda suka sace su.

A baya dai gwamnatinsa ta yi musayar mayakan Boko Haram da wasu daga cikin 'yan matan Chibok.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky