'YAN SHI'A SUN MAKA GWAMNATIN JAHAR SAKKWATO DA JAMI'AN TSARO A KOTU

'YAN SHI'A SUN MAKA GWAMNATIN JAHAR SAKKWATO DA JAMI'AN TSARO A KOTU

'YAN SHI'A SUN MAKA GWAMNATIN JAHAR SAKKWATO DA JAMI'AN TSARO A KOTU

Da safiyar jiya Alhamis ne 23/11/2017. 'Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky na Sakkwato su ka maka Gwamnatin Jahar Sakkwato da Hukumar Jami'an Tsaro a Kotu a bisa zargin da su ke yi na hanasu gudanarda Al'amurran Addininsu kamar yadda su ka fahimta.

Idan ba'a manta ba a kwanakin da su ka gabata Gwamnatin Jahar Sakkwato ta fitar da wata Sanarwa wadda Kwamishinan Shari'a Hon. Barista Suleiman Usman San. Na Jahar Sakkwato ya sanar cewa; Gwamnatin Jahar Sakkwato ta Haramta Ayyukan Mabiya Mazhabar Shi'a a daukacin Jahar Sakkwato, wanda a wannan lokacin wakilin 'yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky na Sakkwato Malam Kasim Umar, ya fito ya yi kira ga Gwamnatin a wannan lokacin kamar yadda su ka sanar cewa sunyi wannan dokar ne saboda su ba mu kariya da cewa bama bukata

Yanzu dai ta baiyana cewa dokar da Gwamnatin Jahar ta fitar da zimmar cewa ta yi ne saboda ta ba mu kariya ba gaskiya ba ne, duba ga irin yadda Gwamnatin Jahar da Jami'an Tsaro su ke amfani da ita gurin muzgunawa tare da sanya Karfi gurin dira akan 'yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H) a Jahar.

Masu Mulki a Jahar Sakkwato sun dade suna amfani da haddasa fadace-fadacen Shi'a da Zauna gari banza domin cimma wadansu gurika nasu na Siyasa.

Babu wata doka ko tsarin Mulkin Kasar nan wanda mu ke takawa a yayin da mu ke gudanarda Al'amurran Addininmu haka kuma dokar kasa ta baiwa ko wane dan Kasa dama ta ya gudanarda Addinin sa kamar yadda ya fahimta matsawar ba zai zama takurawa ga wani ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky