'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 15 a Borno

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 15 a Borno

Wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake sun kai hari kasuwar Biu a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda akalla mutum 15 suka rasa rayukansu, ciki har da 'yan kunar bakin waken.

'Yar kunar bakin wanke ta farko ta tayar da bam din da ke jikinta ne a cikin kasuwar Biu "layin 'yan manja da doya," a cewar wani wanda ya shaida al'amarin.

Sai dai 'yar kunar bakin ta biyu ta ta da bam din da ke jikinta a kusa da kasuwar, wadda take ci a ranar Asabar.

Kakakin rundunar sandan jihar Borno DSP Isuku Victor ya tabbatarwa aukuwar harin, inda ya ce 'yan kunar bakin waken sun kai harin ne da misalin karfe 11:40 na safe a ranar Asabar.

Ya ce bayan mutanen da suka rasa rayukansu, akwai wadansu mutum 53 da suka jikkata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky