Yaki na dab da barkewa tsakanin Koriya ta arewa da Amurka- China

Yaki na dab da barkewa tsakanin Koriya ta arewa da Amurka- China

China ta yi gargadin cewa yaki na dab da barkewa a kowane lokaci tsakanin koriya ta Arewa da Amurka a yayin da kasashen biyu ke wa juna barazana inda China ta yi kiran su kai zuciya nesa.

Ministan harakokin wajen China Wang Yi ne ya yi gargadin a lokacin da ya ke ganawa da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault da ya kai ziyara a Beijing

China ta ce yaki bai taba haifar da nasara ba, illa rungumar tattaunawar fahimtar juna.

Gargadin na China na na zuwa a yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai magance barazanar da Koriya ta Arewa ke yi wa kasar tare da shiga tsakanin China ko kuma Amurkan ta yi ta gaban kanta.

Sannan Trump ya ce yana nazarin daukar matakan soja akan Koriya ta arewa.

Barazanar Trump kuma na zuwa ne a daidai lokacin da Koriya ke shirin gudanar da bukukuwan cika shekaru 105 da haihuwar jagoran juyin juya halinta Kim Il-Sung, yayin da kuma rahotanni ke cewa kasar na shirin yin gwajin wani makami mai linzami a lokacin wannan biki.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky