Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kutsa cikin Jami'ar Maiduguri

Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kutsa cikin Jami'ar Maiduguri

Rundunar 'yansandan jihar Borno ta bada tabbacin wasu 'yan kunar bakin wake sun shiga jami'ar Maiduguri jiya da dare

'Yan kunar bakin waken sun tada bamabaman dake jikinsu a cikin jami'ar kamar yadda kakakin rundunar Victor Osoku ya shaida.

Yace 'yan kunar bakin waken su uku sun nufi dakunan kwanan 'yan mata ne amma basu samu nasara ba domin jami'an tsaro dake aiki cikin jami'ar sun katse masu hanzari.

Dan kunar bakin waken da ya fara tada bam din jikinsa shi kadai ya kashe kansa. Sauran biyun ma da suka tada bamabamansu su ne kadai suka rasa rayukansu. Amma wasu jami'an tsaro dake aiki a jami'ar sun samu raunuka.

Wani ma'aikacin jami'ar yace maharan maza ne kuma su kadai suka mutu. Wani cikin maharan da yayi kokarin sau da kama ya shiga dakin kwanan mata ya fuskanci ihun 'yan matan lamarin da ya sa ya yi ta kare kafin ya tada bam din dake jikinsa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky