Wasu Yan Bindiga Sun Yi Barin Wuta A Cikin Wani Coci A Jihar Anambara

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Barin Wuta A Cikin Wani Coci A Jihar Anambara

Yan bindiga sun kai farmaki cikin wani coci mai suna St. Philips Catholic Church Ozubulu a cikin karamar hukkumar Ekwusigo a jihar Anambara daga kudancin Nigeria a safiyar yau Lahadi.

kamfanin dillancin labaran chinhuwa na kasar China ya bayyana cewa yan bindigan sun shiga cocin ne da misalin karfe 5:45 na safe inda suka kama wani mutum a cikin cocin suka kashe shi a gaban masu addu'a, sannan daga baya suka bude wuta kan mutane kimani 100 da suke cikin cocin. 

Wasu sun mutu nan take a yayinda wadansa suka ji rani masu tsanani kuma suka mutu a kan hanyar kaisu asibitin koyarwa na  Nnamdi Azikiwe dake Nnewi. Kamfanin dillancin labaran NAN na Nigeria ya ce shugaban Cocin bai sami ko korzone ba. 

Kwamishinan yansanda na jihar Anambara Mr Garba Umar ya tabbatar da wannan labarin ya kuma bayyana cewa yana dauke da karin bayani bayan bincike.

Gwamnan jihar ta Anambara Gov. Willie Obiano  ya sha alwashin gano wadanda suka aikata wannan mummunan kisan don a saka masu gwargwadon mummunan aikin da suka yi. Mutane 8 aka tabbatar da mutuwarsu a yayinda wasu 18 kuma suka ji rauni.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky