Wasu ‘Yan Biafra sun yi ikirarin kafa gwamnati

Wasu ‘Yan Biafra sun yi ikirarin kafa gwamnati

Shugaban wata kungiya a kudancin Najeriya da ake kira Biafra Zionist Federation Benjamin Onwuka ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Biafra na riko, tare da zayyana sunayen ministocin sabuwar gwamnatinsa

A yayin da ya ke sanar da matakin a Enugu, Onwuka ya zana sunan Farfesa Chukwuma Solodu a matsayin Gwamnan Babban Banki da Farfesa Pat Utomi a matsayin ministan harkokin waje, da Farfesa Jerry Gana a matsayin ministan sufuri sai Labaran Maku a matsayin ministan sufurin sama da kuma Oruma Oteh a matsayin Ministan kudi.

Akwai Benny Lar da aka nada sakataren gwamnati tare da nada wasu a matsayin jekadun Biafra a Amurka da wasu manyan kasashen duniya.

Mista Onwuka ya ce gwamnatin rikon kwaryar za ta yi aiki ne nan da wata daya daga ranar 1 ga Agusta.

Sannan a cikin sanarwar ya ce Isra’ila ce za ta samar da tsaro a Biafra yayin da kuma kamfanonin Amurka za su tafiyar da harakar arzikin mai a yankin.

Sai dai matakin ya yi karo da kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Biafra ta IPOB inda ta zargi Onwuka da yin zagon kasa ga gwagwarmayar da suke ta tabbatar da kasar Biafra.

Fafutikar kafa kasar Biafra ya taba jefa Najeriya cikin yakin basasa a 1967 zuwa 1970 al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan Miliyan daya.

Wasu Kungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun bukaci Gwamnatin kasar ta gaggauta daukar mataki kan ‘Yan Biafra da suka sanar da kafa Gwamnati.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky