Turkiya Zata Gina Tashar Jiragen Ruwa A Sudan

Turkiya Zata Gina  Tashar Jiragen Ruwa A Sudan

Kasar Turkiya tace zata sake ginawa Sudan tashar jiragen ruwan birnin Ottoman, zalika zata gina sansanin sojin ruwan da zai taimaka wajen samar da tsaro, a wani yunkuri na karfafa alakar soji, da kuma tattalin arziki tsakanin kasashen biyu

Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Gandour, ya bayyana haka ne bayan ziyarar shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya kai zuwa Khartoum.

Yayin gudanar da ziyarar, shugaba Erdogan ya ce Sudan ta baiwa Turkiya wani sashi na gabar ruwan Suakin, domin gina sansanin yawon bude ido, da kuma hanyar tsallakawa zuwa Makkah ga maniyata aikin Hajji.

Matakin na gwamnatin Turkiya ya zo kasa da watanni uku bayan da kasar, ta bude wani sansanin soji da ta gina a kasar Somalia.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky