Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar Masar ya bata

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar Masar ya bata

Habib Adliy tsohon ministan kula da harkokin cikin gidan Masar a zamanin mulkin Husni Mubarak da ke zaman jiran shari'a ya tsere babu labarin yadda ya buya.

Jaridar Almisriyyun a bugunta na jiya Talata ta bada labarin cewa: Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da ma'aikatar shari'ar kasar cewa: Bayan da kotu ta zartar da hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 7 kan tsohon ministan harkokin cikin gidan kasar Habib Adliy kan zargin barnata dukiyar kasa, jami'an tsaro sun neme shi sama da kasa babu labarinsa.

Kafin zartar da hukuncin daurin shekaru 7 kan Habib Adliy kan zargin barnata duniyar kasa, hukuncin da kotu ta zartar kansa dangane da daurin talala a gida, wa'adin hukuncin ya kare, sannan bayan hukuncin karshe na zaman shekaru 7 a kurkuku, an neme shi sama da kasa babu labarinsa, amma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda ya buya.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky