Theresa May: Za mu karfafa alaka da Najeriya bayan ficewa daga Turai

Theresa May: Za mu karfafa alaka da Najeriya bayan ficewa daga Turai

Firaministar Birtaniya Theresa May ta ce Birtaniya da Najeriya za su kara karfafa alakar da za su amfani juna bayan Birtaniyar ta kammala ficewa daga Tarayyar Turai.

Theresa May ta ce tana fatan huldar cinikayya tsakanin kasashen za ta inganta a nan gaba.

Ta bayyana haka ne a Abuja lokacin da ta gana da Shugaba Muhammadu na Najeriya inda suka tattauna kan batutuwan cinikayya da tsaro da safarar mutane da sauransu.

Ta kara da cewa Birtaniya za ta ci gaba da tallafawa Najeriya a bangaren yaki da Boko Haram, da safarar bil adama, da kuma cin hanci da rashawa.

A bangarensa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar ta kallon tsanaki kan abubuwan da suke faruwa a Turai a lokacin da Birtaniya ke ficewa daga tarayyar

Buhari ya kuma godewa Theresa May kan tallafawa kasarsa a bangarori da dama.

Theresa May tana ziyarar ne tare da wata tawagar 'yan kasuwa, inda kuma za a tattauna batutuwan da suka shafi huldar cinikayya tsakanin Birtaniya da Afirka, musamman ma a lokacin da Birtaniya ke gab da ficewa daga Tarayyar Turai.

Tuni dai Theresa May ta bar birnin Abuja zuwa cibiyar kasuwancin kasar Lagos domin tattaunawa da 'yan kasuwa da kuma duba batun safarar mutane.

Dangantakar Burtaniya da kasashen Afirka, musamman ma Najeriya bayan ficewar Burtaniya din daga tarayyar Turai na daga cikin muhimman abubuwan da ake tunanin ziyarar za ta mamaye musamman ganawar da za a yi tsakaninta da shugaba Buhari.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky