Sojojin Somalia na zanga zanga kan albashi

Sojojin Somalia na zanga zanga kan albashi

Daruruwan Sojojin Somalia sun gudanar da zanga zanga a birnin Mogadishu, inda suka tare hanyoyin ababan hawa da tilasta rufe shaguna saboda abinda suka kira rashin biyan su albashi.

Rahotanni sun ce an ga wasu sojojin dauke da makamai suna tare motocin da ke wucewa, yayin da wasu kuma suka bukaci masu shaguna su rufe su.

Captain Ali Osman ya ce sojojin suna tunawa sabon shugaban kasar alkawarin da ya yi cewar idan ya samu nasara zai biya su albashin su.

Wani hafsan sojin da ake kira Mohammed ya ce akalla sojoji 2,000 suka shiga zanga zangar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky