Sojojin Nigeriya Sun Kashe 'Yan Kungiyar Boko Haram Tare Da Kame Wani Kwamandansu

Sojojin Nigeriya Sun Kashe 'Yan Kungiyar Boko Haram Tare Da Kame Wani Kwamandansu

A ci gaba da samamen da rundunar sojin Nigeriya ke gudanarwa a dajin Sambisa babban sansanin mayakan kungiyar Boko Haram, sojojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 4 tare da kame wani daga cikin kwamandojin kungiyar.

Kakakin rundunar sojin Nigeriya Brigadier Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya sanar da cewa: A samamen da sojojin Nigeriya suke ci gaba da gudanarwa da nufin kawo karshen kungiyar Boko Haram; Sojojin kasar sun kai farmaki dajin sambisa da kuma karamar hukumar Kala Balge da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar, inda suka kashe 'yan kungiyar Boko Haram hudu tare da kame daya daga cikin kwamandojin kungiyar mai suna Amma Judee.

Har ila yau a yayin samamen sojojin Nigeriyan sun yi nasarar 'yantar da fararen hula da kungiyar ta Boko Haram ta yi garkuwa da su da yawansu ya kai 212 da suka hada da mata da kananan yara.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky