Sojojin Masar Sun Kashe Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Lardin Sina Ta Arewa

Sojojin Masar Sun Kashe Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Lardin Sina Ta Arewa

Rundunar sojin Masar ta sanar da kashe wasu gungun 'yan ta'adda na mutane bakwai tare da rusa maboyarsu a lardin Sina ta Arewa da ke shiyar arewacin kasar.

A bayanin da kakakin rundunar sojin Masar Tamir Arrafa'i ya fitar yana dauke da cewa: Sojojin gwamnatin Masar sun kai wani samame kan wata maboyar 'yan ta'adda a lardin Sina ta Arewa, inda suka yi nasarar halaka wasu gungun 'yan ta'adda na mutane bakwai tare da rusa hanyar karkashin kasa da 'yan ta'addan suke amfani da ita wajen gudanar da ayyukansu na wuce gona da iri a lardin.

Bayanin rundunar sojin ta Masar ya jaddada shirin cibiyar tsaron kasar na kawo karshen duk wani aikin ta'addanci a kasar musamman lardin Sina ta Arewa da ya zame tungar kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky