Sojoji Zasu yi Juyin Mulki A Nageria?

Sojoji Zasu yi  Juyin Mulki A Nageria?

Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da wasu kalamai da Mataimakin shugaban majalisar dattijan kasar ya yi cewa akwai yiwuwar sojoji su sake kwace mulki a kasar.

Senata Ike Ikweremadu na babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya fadi hakan ne ranar Laraba a zauren majalisar lokacin da yake nuna damuwarsa ga wasu abubuwa da suka faru da yake ganin bai kamata su faru ba a kasar da ke bin tsarin dimokradiyya ba.

"Wa zai ce sojoji ba za su iya dawowa su karbi mulki ba? abu ne mai yiyuwa ga yadda abubuwa ke tafiya a yanzu." a cewarsa mataimakin shugaban majalisar dattijan.

Ya kara da cewa "matsalar da muke fama da ita a Najeriya ita ce dimokuradiyarmu na ja da baya."

Abubuwan da Sanata Ikwerenmadu ya fada da yake ganin sun sabawa dimokuradiya sun hada da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi a Kaduna.

Da kuma yadda aka hanawa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shiga Kano.

"Muna managa kan kwankwaso wanda aka hana wa zuwa jiharsa da ya mulka tsawon shekaru takwas, mun ga mutane dauke da sanduna suna jiransa a filin jirgi".

"Ina maganar yadda jami'an tsaro suka yi wa Dino Melaye kofar rago, yanzu haka a Kaduna, Shehu Sani bai isa ya shirya wani taro ba".

Kuma a haka wani zai ce wai wannan dimokuradiyar za ta dore, ina ganin ba inda za ta je." a cewar Sanata Ikweremadu.

    Amma a sanarwar da rundunar sojin ta fitar a yau Juma'a, ta danganta kalaman a matsayin nuna rashin girmamawa.

Kuma kalaman na iya tasiri ga rage kima da daukakar rundunar sojin ga shugaban kasa da kuma yaddar da ta samu ga jama'a ga kare mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

Rundunar sojin ta kuma fayyace a cikin sanarwar cewa "Rundunar sojin Najeriya yanzu matsayinta ya kai kamar na tsarin kasashen duniya wajen tabbatarwa da kare mulkin demokuradiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky