Shi'a ta roki MDD da ICC kan Zakzaky

Shi'a ta roki MDD da ICC kan Zakzaky

Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta roki Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika da kuma Kotun Duniya da su tsoma baki wajen ganin cewa, gwamnatin Najeriya ta saki jagoransu, Sheik Ibrahim al-Zakzaky da matarsa da ke tsare kusan shekaru biyu.

Shugaban Kwamitin gagwarmayar sakin Zakzaky, Sheik Abdulhamid Bello da ke zantawa da manema labarai a birnin Kaduna ya ce, suna son kuma a tono gawarwakin mabiya Shi’a 347 da aka binne a wani a wani katafaren kabarin bai daya don yi mu su jana’iza irin ta addinin Musulunci.

Sheik Bello ya bukaci kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike game da zargin da suke yi wa sojin kasar kan kisan kiyashin mabiya Shi’a a garin Zaria a shekarar 2015.

A cewar Bello “ ana ci gaba da tsare shugabanmu ba tare da tuhumarsa ba da kuma bada damar ganawa da shi har tsawon shekaru biyu duk da cewa shekara guda kenan da babbar kotu ta bayyana matakin tsare shi a matsayin wanda ya saba doka da keta hakkinsa, sannan kuma ta bada umarin sakin sa ba tare da wasu sharudda ba”.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky