Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci akan Majigin VOA akan Boko Haram

Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci akan Majigin VOA akan Boko Haram

Bayan ya kalli majigin Muyar Amurka Shaikh Dahiru Bauchi ya ce majigin ya nuna a fili muguwar akidar yan kungiyar Boko Haram da suke kashe mutane babu gaira babu dalili

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce nuna majigin aiki ne mai kyau. Yace a nuna wa mutane anfani aikin Alheri. A kuma nuna wa mutane munin aikin sharri. Yace kungiyar Boko Haram sharri ta kawowa duniya. Kamata yayi a nunasu domin a san ayyukansu basu da kyau.

Ya ci gaba da cewa a nisanci irin aikin Boko Haram. Amma kuma idan akwai wadanda suka yi aikin Alheri a nunasu domin a yi kusa dasu a hada kai dasu a aikata aikin Alheri. Y ace Allah yayi gargadin a hada hannu a yi ayyukan Alheri, ayyuka na bautawa Allah da ayyukan da zasu amfani bayin Allah. Amma kada a hada kai akan ayyukan da suka zama ta ta’addanci da kuma cutar da jama’a


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky