Saraki ya fita daga APC

Saraki ya fita daga APC

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana ficewarsa daga jam'iyya mai mulki a kasar, APC.

"Ina sanar da 'yan Najeriya cewa bayan tattaunawa, na yanke shawarar fita daga jam'iyyar APC," in ji shi.

Sai dai kawo yanzu Sarakin bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba tukunna.

Hakazalika Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed shi ma ya bayyana fitarsa daga jam'iyyar, sai dai shi ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Saraki da Gwamna Abdulfatah wadanda tsofaffin 'yan jam'iyyar PDP ne, sun koma jam'iyyar APC ne a shekarar 2014


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky