Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Barazanar Yiyuwar Kai Hare-Haren Ta'addanci A Kasar

Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Barazanar Yiyuwar Kai Hare-Haren Ta'addanci A Kasar

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta kirayi 'yan kasar da kada su daga hankulansu dangane da sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniyya suka fitar na yiyuwar kai harin ta'addancin babban birnin kasar, Abuja da kuma wasu jihohi shida na kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Litinin da ke dauke da sanya hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, Jimoh Moshood, rundunar 'yan sandan ta tabbatar wa al'ummomin wadannan jihohin da kada su daga hankulansu don kuwa tuni ta dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Mr. Moshood ya kara da cewa tuni Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya din Ibrahim Idris, ya ba wa kwamishinonin 'yan sanda da sauran mataimakan sufeto janar din da suke shiyoyi daban daban na rundunar 'yan sandan a duk fadin Nijeriyan da su kara daukan matakan tsaro musamman a wadannan jihohi da ake magana kansu.

A kwanakin baya ne dai ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniyyan suka bayyana cewar akwai yiyuwar 'yan ta'adda su kai hare-hare a wasu yankuna na Nijeriyan da suka hada da birnin Abuja da kuma wasu jihohi shida na Nijeriyan da suka hada da: Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa da kuma Yobe.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky