Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Tura Jiragen Ta Don Neman 'Yan Matan Dapchi

Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Tura  Jiragen Ta Don Neman 'Yan Matan Dapchi

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta kara tura jiragen sama da sauran na'urorin bincike zuwa yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriyan don ci gaba da neman 'yan matan makarantar mata ta Dapchi da suka bace bayan wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar a makon da ya wuce.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya Lahadi ne rundunar sojin saman ta Nijeriyan ta sanar da hakan a kokarin da gwamnatin kasar take yi na gano wadannan 'yan matan da suka bace. Kafin hakan dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya sanar da cewa sojin Nijeriyan za su yi amfani da jiragen sama na leken asiri wajen gano 'yan matan cikin gaggawa.

Wannan sanarwar dai tana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da batar daliban makarantar sakandaren mata na Dapchi din guda 110 wanda ta ce har ya zuwa yanzu ba’aji duriyarsu bayan harin da 'yan Boko haram din suka kai makarantar a ranar Litinin din da ta gabata.

Ministan yada labarai na Nigerian Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a ziyarar da ya kai jihar Yoben a jiya Lahadi karkashin jagoranci wata tawagar ta gwamnatin tarayya a ci gaba da bin lamarin 'yan matan inda ya gana da gwamnatn jihar Yoben Ibrahim Geidam da sauran manyan jami'an gwamnatin.

Gwamnan jihar Yobe din dai ya dora alhakin wannan harin ga rundunar sojin Nijeriyar hakan kuwa saboda janye dakarunta da ta yi ne a yankin wanda hakan ne ya kara wa 'yan Boko Haram din karfin gwiwan kai harin da kuma sace 'yan matan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky