Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Rusa Wani Sansanin Boko Haram A Borno

Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Rusa Wani Sansanin Boko Haram A Borno

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da samun nasarar tarwatsa wani sansani na 'yan kungiyar Boko Haram a yankunan Bukar Meram da kuma Tumbun Allura da ke kusa da Tekun Chadi a jihar Borno.

Daraktan watsa labarai na hulda da jama'a na Operation Lafia Dole na rundunar sojin sama, Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

Sanarwar ta ce an kai hare-haren bayan wasu bayanan sirri da dakarun suka samu dangane da taruwar 'yan ta'addan a wannan wajen da nufin sake kwato wani sansaninsu da aka tarwatsa shi a a farko farkon watan Satumban nan da muke ciki.

Sanarwar ta ce harin da aka kai su da wasu jiragen sama samfurin NAF Alpha Jet da kuma wani jirgin sama mai saukar ungulu na yaki, ya sami nasarar tarwatsa taron na 'yan ta'addan da kashe na kashewa da raunana na raunanawa, tana mai cewa hakan wani shiri ne da dakarun suka dauka na hana 'yan Boko Haram din sake tattaruwa da kuma kokarin kafa sansaninsu.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky