RASUWAR KHALIFA SHEIKH ISIYAKA RABI’U RASHI NE GA DUKKAN ‘YAN NIJERIYA

RASUWAR KHALIFA SHEIKH ISIYAKA RABI’U RASHI NE GA DUKKAN ‘YAN NIJERIYA

RASUWAR KHALIFA SHEIKH ISIYAKA RABI’U RASHI NE GA DUKKAN ‘YAN NIJERIYA
Inji Sheikh Dahiru Usman Bauci

A sakon ta’aziyyah da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fitar jiya da daddare dangane rasuwar Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u ya bayyana wannan rashi na Sheikh Isyaka Rabiu a matsayin rashi ga mahaddata, ‘yan Tijjaniyyah da masu Kudi.
Shehu yace:
 “ Mu mahaddata mun yi rashin mahaddaci, mu ‘yan Tijjaniyyah mun yi rashin dan uwanmu dan Tijjaniyyah, masu kudi sunyi rashin dan uwansu mai kudi. Allah yayi masa gafara ya ji kansa.”
A yayin da Shehu yake bayyana ayyukan alheri da Khalifa yayi a rayuwarshi sai yace:
 “ Ya gina masallatai masu yawa, ya gina makarantu, ya taimaki miskinai da yawa. Allah ya amshi kyawawan ayyukansa Ya yafe masa kurakuransa.”
Shehu ya bayyana cewa suna alfari da Khalifa Isyaka Rabiu cewa a Nijeriya basu da abin alfari kamansa. Shine zai zauna yayi darsu da la’asar. In yayi sallar magariba ya bude wazifa, da safe kuma ya fita Kanti. Ba mai yi wannan sai shi kadai, shine mai darsu, shine muqaddimin bude wazifa, shine kuma mai kayan kamfani a kanti.  A karshe Shehu Dahiru Bauci yayi addu’a akan ruhin Khalifa, sannan yayi addu’a akan Allah ya albarkaci ‘ya’yansa.
Khalifa Shehu Isyaka Rabiu ya rasu ranar Talata, 8/5/2018, a Landan a lokacin da ya je neman magani. Ya rasu yana da shekara 92, ya rasu bar mata uku, da ‘ya’ya fiye da arba’in. Daga cikinshi akwai Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu mai BUA Group, sannan akwai Daha, da Makkiy da sauransu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky