Rashin lafiyar Shugaba Buhari:Sanatoci sun ce Shugaba Muhammad Buhari bai karya wata doka ba

Rashin lafiyar Shugaba Buhari:Sanatoci sun ce Shugaba Muhammad Buhari bai karya wata doka ba

Sanatoci sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai karya wata doka ba na rashin dawowa bakin aiki daga tafiyar da yayi domin ganin likita a kasar Ingila.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashe fiye da kwanaki 90 ba ya kasar nan,yana kasar Ingila domin ganin likitansa,wanda wannan ya haifar da cece-kuce a cikin 'yan kasa da manazarta.
Mai magana da yawun Sanatoci,Sanata Aliyu Sabiu Abdullahi,a wata takarda da ya sanyawa hannu jiya ya bayyana cewa ; "Babu wata doka da shugaban kasa ya karya,saboda haka bai ga dalilin wannan kawar da hankalin  da surutan da ake yi ba.
  "Masu daukan nauyin wannan surutan suna neman suna ne a maimakon zaman lafiyan Nigeriya.
  "Mu da muke majalisar tarayya mun gamsu kuma bamu ga in da aka saba ba.Gwamnatin tarayya tana aiki,kuma mukaddishin shugaban kasa yana yin dukkan abin da ake bugata na shugabanci.Saboda haka babu wani dalili na wannan zanga-zangar da wasu suke yi."
Sanatan yayi kira ga masu wannan zanga-zangar da cewa ; "Saboda haka muna kira ga masu wannan zanga zangar da su dakatar da dukkan wa'yannan zanga-zangugin nasu,su zama masu ruhin 'yan kasanci ta hanyar shiga cikin sauran 'yan kasa masu yin addu'a ga Shugaba Buhari da mukaddishin shugaban kasa da kasar mu Nigeriya a irin wannan mayiwacin hali."
In ba a manta ba,tun shekaranciya litinin ne wasu kungiyoyi suka fara zanga-zanga akan shugaba Muhammadu Buhari ya dawo bakin aiki ko kuma yayi murabus.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky