Palastinawa Na Ci Gaba Da Yajin Cin Abinci A Gidajen Kurkukun Isra'ila

Palastinawa Na Ci Gaba Da Yajin Cin Abinci A Gidajen Kurkukun Isra'ila

Kimanin fursunonin falastinawa 100 ne suka hade da sauran 'yan uwansu masu gudanar da yajin cin abinci a gidajen kurkukun Isra'ila.

Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, Quddurah Faris shugaban cibiyar kula da fursunonin Palastinawa ya bayyana cewa, sakamakon kin karba bukatun Palastinawa masu yajin cin abinci a gidajen kason Isara'ila, wasu karin Falastinawan ma sun bi sahun 'yan uwansu.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Falastinawa 100 ne da suke tsare a wasu gidajen kason Isra'ila suka bi sahun sauran 'yan uwansu, inda su ma suka shiga yajin cin abinci, domin tilsta ma Haramtacciyar kasar Isra'la da ta saurari korafe-korafensu kan rashin kyautata musu a wuraren da ake tsare da su.

Tun fiye da makonni uku da suka gabata ne fursunonin Falastiwan suka fara yajin cin abinci,  inda yanzu adadin masu yajin cin abinci ya kai 1800.

A kasar Afirka ta kudu ma wasu daga cikin 'yan siyasa da suka hada har da wasu 'yan majalisar dokokin kasar sun shiga yajin cin abinci na tsawon sa'oi 24, domin nuna goyon bayansu ga fursunonin falastinawa masu yajin cin abinci, da Isra'ila take tsare da su saboda zalunci da nuna musu fin karfi.

Yanzu haka dai akwai falastinawa dubu 6 da 500 da suke tsare a gidajen kason Isra'ila, da suka hada har da mata 62 da kuma kananan yara da shekarunsu ba su kai a daure su a gidan kaso ba su 300 da suke tsare.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky