Mataimakin Shugaban Najeriya Zai Sanya Hannu Kan Kasasfin Kudin 2017

Mataimakin Shugaban Najeriya  Zai Sanya Hannu Kan Kasasfin Kudin 2017

Mataimakin shugaban kasar Nigeria Yemi Osinbajo Ya ce shi ne zai sanya hannu kan kasafin kudi na wannan shekara ta 2017 idan ya tabbatar da cewa an tsara shi yadda yakamata.

Mukaddashin Shugaban kasar ya bayyana haka ne bayan da ministan watsa Labarai na kasar Lai Muhammad  ya bayyana cewa shi bai san wanda zai sanya hannu a kan kasasfin kudin shekara ta 2017 ba.

Makaddashin  shugaban kasar ya maida martani ne ta bakin kakakinsa Mr Akande, ya kuma bayyana cewa wasikar da shugaban kasa Mohammudu Buhari  ya rubutawa majalisar dokokin kasar a lokacin da zai bar kasar zuwa jinya a birnin London kan cewa mataimakin shugaban kasan zai zama mai kula da al-amuran gwamnati ne kadai ba ta da tasiri a wannan wurin, don tuni tsarin mulkin kasar ya fayyace aikin mataimakin shugaban kasa a duk lokacinda shugaban kasa ya yi balaguro ko kuma ya dauki hutu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky