Masar Ta Jaddada Muhimmancin Dawo Da Kasar Siriya Cikin Kungiyar Arab League

  • Lambar Labari†: 816989
  • Taska : Pars Today
Brief

Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa tun da an kai ga fahimtar cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a kai ga warware rikicin kasar Siriya, to dole ne a dauki matakin dawo da kasar cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa.

A zantawarsa da jaridar Al-Watan ta kasar Masar a jiya Juma'a: Ministan harkokin wajen kasar Samaha Shukri ya jaddada cewa: A halin yanzu an kai ga fahimtar cewa ta hanyar zaman tattaunawa da sulhu ne kadai za a kai ga warware rikicin kasar Siriya da ya kwashe shekaru yana lashe rayukan mutane, to ya zame dole a hanzarta gabatar da shawarar daukan matakin dawo da kasar cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa.

Shukri ya kara da cewa: Wannan shawara tuni ministan harkokin wajen kasar Iraki Ibrahim Ja'afari ya gabatar da ita a zaman taron ministocin kasashen kungiuyar ta hadin kan kasashen Larabawa saboda muhimmancinta, don haka lokaci ya yi da za a ajiye duk wani sabanin mahanga da nufin karfafa hadin kan kungiyar. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky