Majalisar Dokokin Tunusiya Ta Amince Da Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar

Majalisar Dokokin Tunusiya Ta Amince Da Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar

Majalisar Dokokin Tunusiya ta kada kuri'ar amincewa da dukkanin sabbin ministocin da fira ministan kasar ya gabatar mata a matsayin 'yan Majalisun ministocinsa.

A bayan kada kuri'ar amincewa da dukkanin sabbin ministocinsa: Fira ministan Tunusiya Yusuf Sha'hid ya gabatar da jawabi da a ciki ke bayyana cewa: Manufar gudanar da garambawul a Majalisar Ministocin Tunusiya ita ce samar da gwamnati mai karfi da zata bunkasa ci gaban kasar tare da shawo kan matsalar rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa gami da sanya kafar wando daya da ayyukan ta'addanci da kuma barnata dukiyar kasa kafin nan da shekara ta 2020.

Fira minista Yusuf Sha'hid ya kara da cewa: Sabuwar Majalisar Ministocinsa ta kunshi mutane ne da suka shahara a fagen gudanar da ayyukan raya kasa, kuma kwararru da zasu iya samar da canjin da ake bukata cikin gaggawa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky